<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>60</hymn_number>
<title>Maganar Allahnmu Fitila Ce LW60</title>
<lyrics>[V1]
 1) Maganar Allahnmu fitila ce,
 Ta ba da haskenta bisa hanyarmu.
 Ta nuna hanyarmu da za mu bi sosai.
 Ta nuna mugunta, mu yi gudunta.

[V2]
 2)  Maganar Allahnmu wuta ce fa.
 Tana ƙone mugunta, da ƙazanta duk.
 I, ta kan tsarkake zuciyar Masu Bi,
 Haske ya shiga kuwa da murna sosai.

[V3]
 3) Maganar Allahnmu takobi ne,
 Allah ya ba mu shi, mu sari maƙiyi.
 Shaiɗan zai ji tsoron mai riƙon takobin.
 Mun iya kwaƃe shi da maganan nan.

[V4]
 4) Ya ku ƴanuwana, mu yi aniya,
 Tsarkake zuciya da maganarsa.
 Domin mu ƙarfafa, kullum mu karanta
 Littafi Mai Tsarki, ƙyautar Allahnmu</lyrics>
</song>